Tehran Ta Yi Fatali Da Zargin Kasashen Larabawa, Kan Syria

Iran ta yi watsi da zargin da kungiyar kasashen Larabawa ta yi mata kan Siriya, tana mai jadadda son samun zaman lafiya mai daurewa a

Iran ta yi watsi da zargin da kungiyar kasashen Larabawa ta yi mata kan Siriya, tana mai jadadda son samun zaman lafiya mai daurewa a kasar ta Siriya.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ne ya yi watsi da zargin, yana mai bayyana dalilai da dama da suka sa Tehran ke neman zaman lafiya a Syria.

Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a cikin harshen Larabci a shafinsa na X a ranar Juma’a a matsayin martani ga sabuwar sanarwar da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta fitar wacce ke zargin Iran da yin katsalandan a cikin harkokin kasar Siriya.

“Kamar ku, mu ma muna fatan samun kwanciyar hankali, da kuma hana tarzoma da hargitsi a Siriya,” kamar yadda ya rubuta.

Ya ce muna son a kiyaye iyakokin kasar Siriya, bada kariya ga dukkanin kabilu da addinai, da tsaro ga wuraren ibada da kuma takaita mallakar haramtattun makamai.

Hana Syria zama “mafakar ta’addanci”, da kuma tabbatar da cewa Syria ba ta yin barazana ga makwabta da yankin na daga cikin dalilai da ministan na Iran ya bayyana.

Tund afarko dama kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi kakkausar suka da yin watsi da zargin karya da wasu kafafen yada labarai suka yi wa Iran na yin katsalandan a cikin harkokin cikin gidan kasar Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments