Tawagar Majalisar Dinkin Duniya Masu Yaki Da Junansu A Sudan Sun Aikata Laifukan Yaki

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta ce: Bangarorin da suke rikici a Sudan sun aikata laifukan da kan iya zama laifukan yaki Ofishin wanzar

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta ce: Bangarorin da suke rikici a Sudan sun aikata laifukan da kan iya zama laifukan yaki

Ofishin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya tabbatar da cewa: Bangarorin da ke rikici a Sudan sun aikata munanan laifuka na take hakkokin bil adama da kuma laifukan da zasu iya kai wa ga laifukan yaki da cin zarafin bil adama.

Tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakin wasu gagaruman cin zarafin fararen da rusa ababen more rayuwa tare da hana isar da kayayyakin jin kai na bil’Adama ga masu tsananin bukata a sassa daban-daban na Sudan kan Dakarun kai daukin gaggawa da sojojin Sudan da kawayensu.

Tawagar ta kuma jaddada bukatar daukar matakan gaggawa na kare fararen hula, da kuma wajabcin tura rundunar wanzar da zaman lafiya domin kare fararen hula sakamakon irin mummunan halin da suka shiga.

Kamar yadda tawagar ta yi kira da a kara tsananta matakan takunkumin hana shiga da makamai yankin Darfur da suke yaduwa zuwa dukkan sassan kasar Sudan tare da kafa wani tsarin shari’a na kasa da kasa da ke aiki da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya domin yin dubi da binciken matsalolin da suke faruwa a Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments