Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba
Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar da jirgin sama maras matuki ciki na Shahed.
Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na Shahed yana daya daga cikin mafi kyawun nau’ikan jiragen sama marasa matuka ciki a duniya, kasancewar yana da kwarewa sosai wajen ganowa, sa ido da kuma aiwatar da aiki inda ya dace, sannan kuma yana da araha da rahusa.
Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ci gaba da cewa: Babu wani haramcin sayar da jirgin a doka, kuma duk wata kasa da ta yi alkawarin ba za ta yi amfani da shi ba wajen kai wa wata kasa hari, tana iya neman sayan jirgin.