Tawagar kungiyar raya tattalin arziki na kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bar bar birnin Bissau da sauri bayanda shugaban kasa Umaro Sissoco yayi barazanar zai fiddasu daga kasar ida sun kara jinkirin fita.
A cikin watan da ya gabata ne kungiyar ta aiki tawagar zuwa kasar ta Gunea Bissai saboda gabatar da shawarorin kan yadda za’a gudanar da zabubbuka masu inganci a kasar. Tawagar ta kara da cewa tuni ta bawa manya manyan yan siyasa a kasar kofin shawarorin da suka gabatar, sun kuma fara nazarinsu.
Sai dai tawagar ta gaggauta barin kasar a ranar Asabar bayan da ta sami sako daga fadar shugaban kasa mai cewa idan sun ki fita to zai sa a fiddasu da karfi.
Tawagar ta bayyana cewa zata bada rahoto kan abinda suka gani a kasa a kasar ta Guinea Bissau ga shugaban kungiyar tare da shawarar da suka gabatar na yadda za’a gudanar da zabe mai inganci a kasar. Shugaba Embalo dai bai maida martani kan zargin da tawagar ECOWAS take masa ba. A cikin watan watan satumban da ya gabata ne wa’adin shugabancinsa na shekaru 5 ya kare