Tashin Gobara A Tashar Jirgi Ruwa Na Shahid Raja’i Da Ke Kudancin Iran Ya Jikkata Mutane Masu Yawa

Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar

Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran

Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu.

A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu.

Fashewar ta yi karfi sosai, ta yadda mazauna Bandar Abbas da Qeshm suma suka ji karar fashewar.

Daga baya an bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon fashewar tankar mai a tashar ba tare da sanin wani dalili ba, kuma nan take aka aike da tawagogin ma’aikatar bada agajin gaggawa zuwa yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments