Rahotanni daga Siriya na nuni da cewa gomman mutane ne sukayi shahada a sabon rikicin da ya barke a baya baya nan a wasu sassan kasar.
Majiyoyin cikin gida na kasar sun tabbatarwa da tashar Al-Mayadeen cewa, a safiyar Asabar an yi ta kashe-kashe a kauyuka da garuruwa da dama a yankunan karkarar Latakia, Tartous da kuma Hama.
Majiyar ta yi nuni da cewa an yi wani kisan kiyashi a kauyen Al-Sanobar da ke gundumar Jableh.
A cewar wani rahoto na wucin gadi, an kashe mutane 72.
An tabbatar da mutuwar wasu mutane 10 a kauyen Harisoun da ke cikin karkarar Baniyas a cikin gundumar Tartous.
A sa’i daya kuma, kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Syria (SOHR) ta yi nuni da cewa mazauna al’ummar Alawite na cikin fargabar da ke da alaka da yiwuwar kisan kiyashi a kansu daga kungiyoyi masu dauke da makamai masu alaka da gwamnatin al-Jolani.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Syria ta tabbatar da cewa an raba dimbin iyalai daga kauyuka da garuruwan da ke gabar teku, ba tare da wani bayani kan makomar wadannan iyalai ba.
Majiyoyin cikin gida sun ruwaito wa Al-Mayadeen cewa an kashe fararen hula fiye da 400 a kisan kiyashi da kisa a gabar tekun Siriya.
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria ta bayar da rahoton cewa, sama da fararen hula 300 ne aka kashe tun daga ranar alhamis a yayin wani samame da suka kan magoya bayan tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad a yankin gabar tekun yammacin kasar.