Taron na musamman na kungiyar hadin kan Larabawa don tallafawa Gaza

A yau Alhamis kungiyar hadin kan Larabawa za ta gudanar da wani zama na musamman domin yin nazari kan “manufofin magance laifukan kisan kare dangi

A yau Alhamis kungiyar hadin kan Larabawa za ta gudanar da wani zama na musamman domin yin nazari kan “manufofin magance laifukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a kan al’ummar yankin zirin Gaza.

Muhannad al-Akluk, wakilin Falasdinu a kungiyar hadin kan Larabawa ya sanar da cewa: Bisa la’akari da yadda Isra’ila ke ci gaba da aikata laifukan kisan kare dangi a kan al’ummar Palastinu a cikin watanni 9 da suka gabata, da kuma la’akari da hankoron da gwamnatin mamaya ke yi na hana ‘yancin kan Falastinu, kungiyar hadin kan Larabawa za ta gudanar da wannan taro domin nazarin matakan da kasashen Larabawa za su dauka.

Ya kara da cewa: A cikin wannan taro za a yi nazari kan fadada matsugunan yahudawan sahyoniya da kuma tauye ikon gwamnatin Palasdinawa da kuma take-taken  gwamnatin sahyoniya kan kadarorin gwamnatin Falastinu.

A bangare guda kuma, “Tlalang Mofokeng”, wakilin musamman na MDD kan harkokin kiwon lafiya, ya bayyana cewa, abin da ke faruwa a zirin Gaza babu shakka kisan kiyashi ne, kuma babu wani suna da za a iya kiran hakan da shi wanda ba kisan kiyashi ba.

A baya kakakin UNRWA Louis Wateridge ya yi Allah wadai da mawuyacin halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza cikin watanni 9 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments