A yau Juma’a ne aka bude taron kasashen Iran, Rasha da China, a matakin mataimakan ministocin harkokin waje inda su ka tattauna shirin makamashin Nukiliya na Iran. Mahalarta taron sun bukaci ganin an dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata, sannan kuma a warware batun shirinta na makamashin Nukiliya ta hanyar tattaunawa. Kasashen na China, Rasha da kuma Iran sun bayyana takunkuman na Amurka akan Iran da cewa, ba halartattu ba ne.
Haka nan kuma sun ce; Tuntubar juna da kuma tattaunawar diplomasiyya bisa girmama juna ne kadai zabin da ake da shi domin cimma manufa.
Taron da aka yi a yammacin birnin Beijing ya kunshi mataimakan ministan harkokin wajen Iran Garid Ridh Abadi, Sai Rasha Sergey Ryabkov da kuma mai masaukin baki na China Ma Zhaoxu.
A daya gefen kasashen uku sun tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakaninsu a karkashin kungiyoyin kungiyoyin “Shanghai” da kuma “Brikcs”.