An bude taron farko na ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Sahel (AES) a wannan Litinin, a birnin Bamako, na kasar Mali.
Taron wani muhimmin mataki ne na aiwatar da bangaren “Diflomasiyya” na kungiyar, daya daga cikin muhimman ginshikan kungiyar AES, da nufin ayyana ayyuka da matakan da suka wajaba don karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar.
Wannan taron, wanda ya yi daidai da cika shekara guda da rattaba hannu kan Yarjejeniya ta Liptako-Gourma, wacce ta kai ga kafa kungiyar AES.
Ministocin sun yi nazari kan manyan batutuwa da suka shafi kasashen, musamman daftarin farko na dokokin cikin gida da kungiyar hadin kan kasashen Sahel, da kuma kara daidaita ayyukansu na diflomasiyya.
A yayin jawabinsa, ministan harkokin wajen Nijar Bakary Sangare, ya yaba gagarumin ci gaban da aka samu a fannin tsaro, musamman samar da rundunar hadin gwiwa da kuma nasarorin da sojoji suka samu.
Dangane da bangaren ci gaba, ana kokarin hada albarkatun tattalin arziki da inganta masana’antu da ababen more rayuwa, tare da yin la’akari da tsara ayyukan da za a samar da kudaden raya kasa, inji shi