Search
Close this search box.

Tarayyar Turai Ta Bada Taimakon Euro Biliyon 43 Ga Kasar Ukraine Don Ci Gaba Ya Yaki A Rasha

Jami’i mai kula da al-amuran harkokin wajen tarayyar Turai Josept Borrel, ya bada sanarwan cewa kasashen kungiyar sun yanke shawarar bada Euro biliyon 43 ga

Jami’i mai kula da al-amuran harkokin wajen tarayyar Turai Josept Borrel, ya bada sanarwan cewa kasashen kungiyar sun yanke shawarar bada Euro biliyon 43 ga kasar Ukraine don tallafa mata a yakin da take fafatawa da kasar Rasha.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Borel yana fadar haka bayan taron ministocin tsaro na kasashen kungiyar EU a birnin Brussels.

Borrel yaa kuma kara da cewa, daga cikin kadarorin kasar Rasha da suka kwace a kasashen na Turai har yanzun ba su sami damar aika wa Ukraine Euro biliyon 6.6 da yakamata su aiko mata ba.

Daga karshen jami’in ya kara da cewa yakin da Ukraine take fafatawa da Rasha barazana ce ga kasashen kungiyar tsaro ta NATO don haka dole ne kasashen su zaje dantse don tabbatar da cewa Ukraine ta sami nasara a yakin da take fafatawa da kasar Rasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments