Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli.
“Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu yi hakan,” in ji shi.
Sai dai ya jaddada bukatar yin taka-tsan-tsan don tabbatar da cewa babu wanda zai yi amfani da shawarwarin bangarorin biyu a matsayin wata hanya ta cimma burins ana siyasa.
Ya bayyana fatan cewa kasashen Turai uku za su fahimci cewa “idan manufar ita ce cimma yarjejeniya mai ma’ana tsakanin bangarorin biyu, to komai mai yiwuwa ne.”