Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa ya jadadda cewa; Diflomasiyya ita ce mafita ga amfanin kowa, kuma yaƙi caca ce da ba za a iya sarrafa ta ba
Majid Takht-Ravanchi, Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran kan Harkokin Siyasa, ya bayyana cewa: Mayar da hankali kan diflomasiyya yana da amfani ga kowa, yana mai gargadin cewa “idan yaki ya barke, ba za a iya shawo kansa ba, kuma daga mahangarsu, caca ce ta gaske.”
A wata hira da ya yi da NPR, Takht-Ravanchi ya kara da cewa: “Babu mafita ta soja ga batun makamashin nukiliyar Iran,” yana mai jaddada cewa: diflomasiyya, ba tashin hankali ba ce, ita ce hanya mafi kyau ta daukar mataki.
Ya bayyana cewa: Maimakon fadada karfin soja da tura sojoji da jiragen ruwa zuwa yankin, ya kamata a mayar da hankali kan hanyar diflomasiyya, domin ita ce kawai hanyar magance matsalolin da za su dore.
Majid Takht-Ravanchi ya sanar da shirin Iran na cimma yarjejeniya da wuri-wuri, yana mai tabbatar da cewa kasarsa za ta shiga tattaunawar Geneva da gaskiya da kuma kyakkyawar manufa. Ya kuma jaddada muhimmancin samun martani mai kyau da gaskiya daga bangaren Amurka don cimma wannan burin.