Tashar talbijin din ‘almayadin’ mai watsa shirye-shirye daga Lebanon ta ambaci cewa; Wasu kauyuka na mabiya mazhabar Alawiyya dake Tartus, da kuma Lazikiyya, sun fuskanci hare-hare daga masu dauke da makamai.
A yau Lahadi, masu dauke da makaman sun kutsa cikin wasu kauyukan Ramilah, Naq’a dake kusa da Jabalah.
Daga jiya zuwa yau masu dauke da makaman sun yi kisan kiyashi a wurare fiye da 10.
Majiyar Almayadin ta ce ya zuwa yanzu adadin wadanda aka kashe bisa bangaranci sun kai 1000.
Sai dai kuma tshohon mai bai wa shugaban majalisar ‘yan Alawiyya shawara Muhammad Nasir, ya ce, adadin wadanda aka kashe din sun kai 1,700.
Hare-haren sun hada da kona kauyuka 6 a yankin gabar ruwan Midtreniya na kasar Syria.
Da akwai wasu daruruwan gawawwaki a kwance akan titunan garuruwa da kauyuka da biranen yakin Lazikiyya da Hasakah.
A cikin wasu kauyukan mutane da dama sun gudu zuwa kan duwatsu da dajuka domin su tsira da rayukansu.