Sudan Ta Kudu, Ta Kara Tsawaita Wa’adin Mika Mulki Zuwa 2026

Sudan ta Kudu ta kara tsawaita mika mulki a siyasance tare da dage zabenta har zuwa karshen shekarar 2026. Da farko an shirya yin zaben

Sudan ta Kudu ta kara tsawaita mika mulki a siyasance tare da dage zabenta har zuwa karshen shekarar 2026.

Da farko an shirya yin zaben a watan Disamba 2024, don haka za a gudanar da zaben a watan Disamba na 2026.

Gwamnatin kasar ta sanar da hakan ne da yammacin jiya Juma’a, bayan wani taron fadar shugaban kasar da ya hada shugaba Salva Kiir, da kuma mataimakansa guda biyar.

Fadar shugaban kasar ta sanar a shafinta na Facebook, cewa saboda bukatar da ake da ita na samar da karin lokaci don aiwatar da “ayyuka masu muhimmanci” na yarjejeniyar zaman lafiya, na daga cikin dalilan dage zaben.

Ministan harkokin majalisar ministocin kasar Martin Elia Lomuro ya ba da hujjar dage zaben bisa “shawarwari daga cibiyoyin zabe da kuma bangaren tsaro”, da kuma “mahimman ayyukan da suka dace don gudanar da zabukan cikin sauki”.

Ko a shekarar 2022 Sudan ta Kudu ta dage zaben kasar da shekara biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments