Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sudan sun ce rundunar kai daukin gaggawa mai fada da sojojin kasar Sudan ta kai wa garin “Tandalti” hari da jirgen sama marasa matuki jim kadan bayan ziyarar shugaba majalisar shugabancin kasar Janar Abdulfattah al-Sisi.
Majiyar sojan kasar Sudan ta ce, sun yi amfani da na’urorin kakkabo jiragen sama, akan hare-haren na rundunar kai daukin gaggawa tare da kakkabo da dama daga cikinsu.
Wadannan hare-haren dai sun faru ne jim kadan bayan wata ziyara da shugaban majalisar shugabancin kasar ta Sudan janar Burhan Abdulfattah ya kai garin “Um-Ruwabah’ wanda sojojin Sudan din ba su dade da kwato shi ba.
A cikin makwannin bayan nan dai sojojin na Sudan suna cigaba da samun nasara akan dakarun kai daukin gaggawar tare da kwace garuruwa masu muhimmanci daga wurinsu.
Sojojin na Sudan sun kori mayakan dakarun kai daukin gaggawa daga cikin yankin Aljariza dake kusa da babban birnin kasar ta Khartum.
A gefe daya wata kungiya ta likitocin kasar ta Sudan ta sanar da cewa mutane 61 su ka rasa rayukansu sanadiyyar harin da rundunar kai daukin gaggawa ta kai wa kasuwar birnin Umdruman, yayin da wasu mutanen masu yawa su ka jikkata wasu da dama.