Tashar talabijin din al-mayadin ta bayar da labarin cewa, rundunar kai daukin gaggawar ta kai hari akan masallacin unguwar “Abu Shauk” dake birnin Al-fasha a lokacin sallar asuba.
Da safiyar jiya juma’a ne dai mayakan rundunar ta r.s.f su ka kai wa masallacin na Abu Shauka hari a birnin al-fasha da shi ne babban birnin gundunar Darfur ta Arewa.
Mutane 75 ne su ka yi shahada sanadiyyar wannan harin da aka bayyana a matsayin kisan kiyashi.
Wata majiya a garin da aka kai wa harin, ta ambaci cewa wadanda suke salla a masallacin ‘yan hijira ne da aka koro daga yankunan da yaki ya yi tsanani.
Kwamitin da yake kula da kungiyoyin dake fada da rundunar rsf ya ce; An yi amfani da jirgin sama maras matuki ne wajen kai wa masallacin hari.
A baya kwamitin bincike na MDD ya zargi rundunar kai daukin ggagawa da tafka laifi akan bil’adama. Ta kuma zargi rundunar da cewa yana hana mutane samun abinci,kuma tana lalata asibitoci.