Sojojin Sudan suna ci gaba da bata-kashi da dakarun rundunar kai daukin gaggawa a yammaci da kudancin birnin Umdurman.
Majiyar gwamnatin Sudan ta fada wa manema labaru cewa; An dauke mazauna yankin da ake fadan a birnin Umdurman da adadinsu ya kai 5,000 zuwa arewacinsa.
A lokaci daya kuma sojojin na Sudan suna ci gaba da abinda su ka kira da “Shara” a yankin “Jabalul-Auliya” dake kudancin birnin Khartum.
A can birnin Al-Fasha, jiragen saman sojojin Sudan suna kai hare-hare akan wuraren dakarun kai daukin gaggawa a cikin birnin, da hakan ya haddasa asarar ta rayuka da kuma kayan yanki.
A cikin kwanakin bayan nan sojojin Sudan suna samun nasara akan dakarun kare daukin gaggawa da ya hada da korarsu daga birnin Khartum da wasu muhimman birane da su ka hada da Jazira.
Tun a cikin watan Aprilu na 2023 ne dai kasar Sudan ta fada cikin yakin basasa, bayan da dakarun rundunar kai daukin gaggawa su ka mamaye wasu cibiyoyin gwamnati.
Ya zuwa yanzu dai adadin wadnada su ka rasa rayukansu sun wuce 20,000, yayin da wasu miliyan 15 su ka zama ‘yan hijira.