Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da kungiyar al-Shabaab ta kai a wani otel da ke garin Baledweyne, inda shugabannin kabilu ke ganawa ya kai mutane 10, kamar dai yadda majiyoyin ‘yan sanda na kasar ta Somalia suka tabbatar.
Sannan kuma bayanin hukumar ‘yan sandan ta kasar Somalia ya tabbatar da cewa, akasarin wadanda suka rasa rayukansu fararen hula ne.
A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani otel da ke birnin Baledweyne da wata mota da aka shakare da bama-bamai, kafin daga bisa suka shiga cikin otal din suka kai farmakin da ya dauki tsawon yini guda.
Majiyoyin ‘yan sandan sun tabbatarwa kamfanin dillanmcin labaran Reuters cewa, hudu daga cikin ‘yan ta’addan sun tarwatsa kansu, yayin da kuma jami’an tsaro suka halaka biyu daga cikinsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Al-Shabaab kungiyar da ke da alaka da Alqaida, ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce mayakanta sun kashe mutane 20 da suka hada da sojoji da shugabannin kabilu.
Shugabannin kabilu daga yankin Hiran sun hallara a otal din domin tattaunawa kan yadda za a tunkari ayyukan ta’addancin kungiyar Al-Shabaab da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al’ummar kasar.