Sojojin kasar ayemen sun kakkabo jiragen yaki na kasar Amurka wadanda ake sarrafashi daga nesa a kan kasar Yemen, da dama wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon $200 a cikin makonni 6 kacal.
Tashar talabijin ta Pressstv a nan Tehran ya bayyana cewa wadan nan jiragi suna aikin leken asiri ne a kan kasar ta Yemen, kuma duk da cewa suka tashi fiye da kafa 40,000 a sama, amma sojojin yemen suna iya kakkabosu.
Wannan yana zuwa ne a dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donar Trump ya kara umurnin a kara yawan hare-haren da ake kaiwa kasar ta Yamen.
Mafi yawan hare-haren da suke kaiwa yana kasa mata da yara da kumalalata kamfanoni da kuma cibiyoyin samar da ruwa ko ajiyar makamashi ne .
Don haka hare-haren basa kaiwa ga makaman sojojin kasar Yemen wadanda suke karkashin kasa kuma nesa daga inda makaman Amurkka zasu samesu.
Amurka dai ta fara yake da Yemen ne don tallafawa HKI kan hare –haren sojojin yemen kanta tun baya sake dawoda yakin dofan al-aksa.