Sojojin Yemen sun kai hari kan jirgin ruwan Amurka kirar “Harry Truman” mai dakon jiragen sama
Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya fitar da wata sanarwa a yammacin jiya Asabar cewa: Sun kai hari kan jirgin ruwan Amurka USS Harry Truman da wasu jiragen ruwan yakinsu a yankin arewacin tekun Bahar Maliya da wasu makamai masu linzami da jirage marasa matuka ciki.
Yahya Sari’e ya jaddada cewa: Hare-haren suna zuwa ne a matsayin taimako ga al’ummar Falastinu da ake zalunta tare da mayar da martani kan kisan kiyashin da ake yi wa ‘yan uwansu a Gaza, da kuma harin baya-bayan nan da Amurka da Birtaniya gami da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen.