Sojojin kasar Yemen sun kai hari kan filin sauka da tashin jiragen Sama na Ben Gurion na haramtacciyar kasar Isra’ila
Rundunar sojin Yemen ta sanar da kai wani harin makami mai linzami kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye, inda ta sanar da samun nasarar farmakin. Har ila yau, sojojin Yemen sun kai hari kan wasu wurare biyu na gwamnatin mamayar Isra’ila a Jaffa da Ashkelon da jiragen sama marasa matuka ciki.
Dakarun Yaman sun sanar da yammacin jiya Juma’a cewa: dakarun sojojin kasar masu kula da makamai masu linzami sun kai wani harin soji kan tashar jirgin saman Lod (Ben Gurion) da ke yankin Jaffa da aka mamaye, ta hanyar amfani da makami mai linzami na “Palestine 2”.
A cikin sanarwar, kakakin rundunar sojan kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa makamin ya ratsa na’urorin kakkabo makamai masu linzamin gwamnatin mamayar Isra’ila tare da samun nasarar cimma burinsa. Ya yi nuni da cewa, aikin ya haifar da rudani a tsakanin makiya, wanda ya tilasta wa miliyoyin yahudawan sahayoniyya tserewa zuwa maboyar karkashin kasa da kuma dakatar da ayyukan tashar jirgin.