Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila
Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma wasu muhimman wurare a yankunan Jaffa, Ashdod da Umm al-Rashrash a cikin Palasdinu da aka mamaye.
Rundunar sojin Yemen ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau cewa: Rundunarta ta kai wasu hare-haren soji masu inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami.
Dakarun sojin sun tabbatar da cewa: wannan farmakin ya samu nasarar cimma burin da aka sanya a gaba, wanda ya sa miliyoyin garken yahudawan sahayoniyya suka tsere zuwa maboyar karkashin kasa tare da janyo dakatar da ayyukan tashar jirgin saman.
Dakarun sojin Yemen sun yi nuni da cewa: Jiragen saman yaki mara matuki sun kai farmakin soji guda uku, inda suka auna wasu muhimman wurare uku na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan Jaffa, Ashdod, da Umm al-Rashrash da ke yankin Falasdinu da aka mamaye, ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda uku.