Sojojin Yemen Sun Kai Farmaki Kan Tashar Jiragen Sama Na Bengerion A HKI

Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare da makamai masu linzami kan tashar Jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) a safiyar yau

Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan kai hare-hare da makamai masu linzami kan tashar Jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) a safiyar yau Laraba. Kuma makaman sun sami inda ake bukata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa sojojin sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin Bilistet a hare-haren, kuma sun kaisu ne tallafawa Falasdinawa a Gaza wadanda HKI takewa kissan kare dangi.

Labarin ya kara da cewa daya daga cikin makamai masu linzamin ya sami tashar jiragen kai tsaye ba tare da an kakkabishi ba.

Makaman sun hargitsa zirga-zirgan jiragen sama, a tasahr na wani lokaci sannan ya sa yahudawa tsakiyar Yafa (Telaviv) da yankin yamma da kogin Jordan da birnin Qudus shiga wurarenn fakewa.

Sannarda Burgediya Yahyah Saree ya bayyana ya kara jadda haramta sauka da tashin jiragen sama a tasahr sannan ya yi kira ga dukkan jiragen sama su dakatar da zuwa zuwa tashar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments