Mai Magana da yawun mutanen kasar Yemen Burgedia Yahyah Saree ya bayyana cewa sojojin kasar sun cilla makamai masu linzami kan katafaren jirgin yaki mai daukar jiragen sama mallakin kasar Amurka a tekun Red rea kuma makamin ya sami bararsa kamar yadda ake so.
Tashar talabijin ta Al-Alam ta bayyana cewa majiyar Pentagon ko kuma gwamnatin Amurka ta yi gam da bakinta kan wannan labarin har yanzu basu fadi kome. Amma hotunan da kasar China ta dauka na jirjin a tekun Redsea ya nuna inda makamai masu linzami na kasar Yemen suka fada a kan jirgin da kuma babban ramin da makaman suka haddasa a kan jirgin.
Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa a halin yanzu jirgin yana kasar Saudiya mai yuwa don gudanar da gyarengyare a wuraren da suka lalace a jirgin. Kuma ba’a san zuwa yauce ne za’a kammala aikin gyaran ba.