Sojojin Yemen Son Kai Hare Hare Kan Sojojin HKI Saboda Tallafawa Mutanen Gaza Da Kuma Lebanon

Kakakin sojojin kasar Yemen Yahya Sarii ya bayyana cewa bangaren makamai masu linzami na sojojin kasar Yemen sun cilla makamai masu linzami samfurin Quds 5

Kakakin sojojin kasar Yemen Yahya Sarii ya bayyana cewa bangaren makamai masu linzami na sojojin kasar Yemen sun cilla makamai masu linzami samfurin Quds 5 kirar cikin gida  kan sansanin sojojin HKI a safiyar yau Laraba. Kuma sun kai hare haren ne don tallafawa al-ummar Falasdinu wacce ake zalunta a Gaza da kuma mutanen kasar Lebanon.

Yayah Saree ya bayyana haka ne a wata sanarwan da ya bayar kai tsaye ta tahsar talabijan ta kasar dake birnin san’aa.

Kakakin sojojin kasar ta Yemen ya kara da cewa makamai masu linzamin sun fada kan wuraren da aka tsara zasu fada. Sai dai HKI tana boye asarorin da take yi, don haka basa barin a watsa duk asarar da suka yai.

Yahya Saree ya kammala  da yabawa JMI da hare haren waadussadik 2 da ta kai kan HK a jiya Talata, ya kuma ce, sojojin kasar Yemen a shirye suke su aike da sojoji don yakar gwamnatin HKI a duk sanda bukatar hakan ta taso.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments