Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar da fara wani gagarumin farmakin soji a yammacin gabar kogin Jordan
Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da hukumar tsaro tayahudawan sahayoniyya “Shin Bet” sun sanar da fara wani gagarumin farmaki ta hadin gwiwa a yankunan Gabar yammacin kogin Jordan a yau Laraba, inda suka kaddamar da hare-haren soji kan garuruwan Jenin da Tulkaram dake gabar yammacin kogin Jordan.
Majiyoyin yankin na Falasdinawa sun yi nuni da cewa: Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun fara kai wani gagarumin farmaki a garuruwan Jenin, Tulkaram da kuma sansanin Al-Faraa da ke Tubas.
Majiyoyin sun kara da cewa: Sojojin mamayar suna killace asibitocin Falasdinawa a birnin Tulkarm da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan. Kamar yadda kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka sanar da cewa: Daruruwan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ne suka fara gudanar da samame a shiyar arewacin gabar yammacin kogin Jordan, tare da samun tallafin jiragen saman yaki.
A nata bangaren, jaridar yahudawan sahayoniyya ta Yedioth Ahronoth ta ce: Sojoji mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun killace asibitoci a Tulkarm da Jenin a wani bangare na fadada ayyukansu.