Dakarun Izzudden Qassun reshen soje na kungiyar Hamas ya bada labarin cewa wani daga cikin dakarunsu ya tarwatsa kansa da damarar boma-bomai a unguwar Tel Za’atar a cikin yankinnan yamma da kogin Jordan, tare da nasarar halaka dukkan sojojin yahudawa 5 da yake hara.
Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Qassam na cewa, bayan isowar tawagar masu ceton yahudawan wurin da abin ya faru sun farmasu da barin wuta wanda ya halaka wasu daga cikinsu.
A birnin Tel-aviv kuma wani matashi dan shekara 28 a duniya ne, ya caccakawa wata bayudiya diyar shekara 80 a duniya wuka wanda ya kaita ga halaka, amma sojojin yahudawan sun kashe shi nan take, suka kuma tafi da gawarsa.
Labarin ya kara da cewa wadannan al-amura sun faru ne a safiyar yau Jumma’a, wadanda kuma suka rikata harkokin tsaro a cikin HKI.