Sojojin Sudan Sun Yi Luguden Wuta Kan Fararen Hula A Kasuwa A Yankin Darfur Ta Arewa

Jiragen saman yakin sojojin Sudan sun yi luguden wuta kan wata kasuwa da ke arewacin Darfur lamarin da ya janyo mutuwa da jikkatan daruruwan mutane

Jiragen saman yakin sojojin Sudan sun yi luguden wuta kan wata kasuwa da ke arewacin Darfur lamarin da ya janyo mutuwa da jikkatan daruruwan mutane

Rahotonni sun bayyana cewa: Hare-haren da jiragen saman yakin sojojin Sudan suka kai kan yankin arewacin Darfur sun yi sanadiyyar mutuwa da jikkatan daruruwan mutane fararen hula.

Kungiyar lauyoyin kai daukin gaggawa da ke tattara bayanan dangane da batutuwan take hakkin bil adama a lokacin yakin da ake yi a kasar, ta ce; Jiragen saman yakin sun kai hare-haren ne kan birnin Kabkabiya da ke arewacin Darfur, inda ya afka cikin wata kasuwa mai cike da dimbin jama’a da suka taru domin yin sayayya.

A wani labarin kuma, kungiyar ta ce wani jirgin sama maras matuki ciki ya yi hatsari a jihar Arewacin Kordofan da ke tsakiyar kasar ta Sudan, inda ya kashe mutane shida ciki har da kananan yara, yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments