Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar
Rundunar sojin Sudan ta sanar a yau jiya Talata cewa: Sojojinta da mayakan da suke goya musu baya sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar, kuma babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar Janar Abdul-Fattah Al-Burhan ya yi alkawarin samun nasara a nan kusa kadan kan wadanda ya kira ‘yan tawaye.
Sojojin Sudan sun watsa labarin ta hanyar kafofin Facebook da Instagram tare da wallafa faifan bidiyon yadda al’ummar birnin suka fito kan tituna suna bayyana murnarsu da ‘yantar da birninsu daga hannun ‘yan tawaye tare da bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba ga sojojin Sudan.
A nasa bangaren, shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan, kuma babban hafsan hafsoshin sojin kasar Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan ya ce: Sojoji na gab da kammala samun nasara bayan da suka fatattaki Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces a dukkan yankunan birnin Khartoum fadar mulkin kasar.