Sojojin Sudan Sun Fatattaki Dakarun Kai Daukin Gaggawa Daga Sansaninsu Da Ke Birnin Omdurman

Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakan ‘yan tawayen kasar na kungiyar Rapid Support Force daga sansanoninsu da ke kudancin Omdurman Hukumomin sojin Sudan a birnin

Sojojin Sudan sun yi nasarar fatattakan ‘yan tawayen kasar na kungiyar Rapid Support Force daga sansanoninsu da ke kudancin Omdurman

Hukumomin sojin Sudan a birnin Omdurman na jihar Khartoum, sun sanar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun tsare sun bar makamai da alburusai da dama da suka hada da haramtattun makamai da aka hana amfani da su a dokokin kasa da kasa, bayan da suka sha kashi a yankin Al-Saliha da ke kudancin birnin. Majiyoyin sun kuma tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawan suka kwace gidajen zaman jama’a da karfi da yaji domin amfani da su a matsayin ma’ajiyar makamai.

Yakin baya- bayan nan da sojojin Sudan suka yi da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces a yankin Al-Saliha da ke kudancin Omdurman ba abu ne mai sauki ba. An kwashe sama da wata guda ana gwabza fada. Babban dalilin shi ne mallakar manyan makamai da Dakarun kai daukin gaggawa suka yi, wanda ya janyo bullar tambayoyi da dama kan yadda dakarun da ba su da isasshen horo don amfani da irin wadannan makaman za su iya mallakar su, sai dai idan suna samu goyon baya daga waje.

Suleiman Abdo Ali, kwamandan rundunar soja ta Takht Omdurman, ya ce: “Alhamdu lillahi, an fatattaki makiya sun bar kayan aikin soja, da a ce sun kasance sojoji ne na yau da kullun ko kuma sojoji ne masu manufa ko wata akida da su tsaya a fafata da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments