Search
Close this search box.

Sojojin Sahayoniyya Sun Kashe Falasdinawa Da Koran Wasu 250,00 Daga Muhallinsu A Deir Al-Balah

An samu shahadan Falasdinawa tare da raunata wasu a Gaza tare da tilastawa wasu kimanin 250,000 gudun hijira a Deir al-Balah Majiyoyin lafiya a Gaza

An samu shahadan Falasdinawa tare da raunata wasu a Gaza tare da tilastawa wasu kimanin 250,000 gudun hijira a Deir al-Balah

Majiyoyin lafiya a Gaza sun sanar da shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkata wasu masu yawa sakamakon hare-haren kisan kiyashin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan yankuna da dama a Zirin Gaza tun daga wayewar garin ranar Litinin.

Har ila yau wasu Falasdinawa da dama sun yi shahada a harin da aka kai kan wata makaranta mai dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin Nuseirat. a cikin tsakiyar Gaza.

Kamar yadda a gefe guda kuma, mayakan rundunar Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas suka watsa hotunan wani gagarumin harin kwantan bauna da suka kai kan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda suka tarwatsa wasu gungun sojoji da suka killace wani gida da ke gabashin Khan Yunus.

Dangane da kashe-kashen da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, sojojin sun ci gaba da aikata laifukan da suka shafi fararen hula tare da raba Falasdinawa da matsugunansu a duk fadin yankin Zirin Gaza.

A arewacin zirin Gaza kuwa, inda har yanzu sojojin mamaya ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, majiyoyin Falasdinawa sun ce an samu hasarar rayuka da dama a kan hanyar Al-Hoja a sansanin Jabaliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments