Sojojin kasa na jumhuriyar Musulunci ta Iran sun hada guiwa da sojojin ruwa don atisayen hadin guiwa wanda suka sanyawa suna Zulfikar 1403.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakain atisayen Brigadier General Alireza Sheikh yqana cewa a cikin wannan atisayen suna son gwada aiki tare da sojojin masu aiki a sama da na ruwa don samar da yanayi irin na yanayi yaki da gaske don fahintar da harkokin yaki suke tafiya.
General Alireza Sheikh yace a bangare na farko na wannan atisayen mun gwada yadda jiragen yakin masu saukar ungulu zasu sauka su tashi a dai dai lokacinda ake cikin budewa juna wuta da makiya.
Sannan manufar atisayen gaba daya itace samar da yanayi ta yadda bangarorin sojojin kasar zasu yi aiki tare a lokacin yaki, ko wane bangare yana aiki a bangaren da ya kore a kai amma kuma suna yakar makiyi guda.
Ya ce zasu yi amfani da jiragen yaki masu saukar ungulu, jiragen yaki na sojoji, masu saukar ungulu nau’in Cobra RH, SH da kuma AB212.. Sannan ana wannan atisayen ne a tashar jiragen ruwa na sojojin kasar dake Makron. Gabaki dayan atisayen na karkashin shi’arin Zulfikar 1403 ne.