Falasdinawa fiye da 50 ne suka yi shahada yayin da wani adadi da dama suka jikkata a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai Gaza a jiya Litinin
Rahotonni sun bayyana cewa: Fiye da Falasdinawa 50 ne aka suka yi shahada wasu adadi da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu. Daga cikin hare-haren har da hare-haren da jiragen mamayar Isra’ila suka kai kan wani gini mai yawan jama’a a unguwar Al-Karama da ke arewacin Gaza, wanda ya yi sanadin kisan kiyashi kan mutane ciki har da mata da kananan yara 20 da kuma fararen hula na daban.
A wani labarin kuma, Falasdinawa a yankin Al-Karama da ke arewacin zirin Gaza sun farka da wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi bayan da suka kai hari kan wani ginin fararen hula, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkata.
A tsakiyar daren jiya ne jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai hare-hare kan wani gini mai hawa uku, inda suka yi sanadiyyar shahada Falasdinawa kusan 20, kuma har yanzu ba a gano wasu gawarwakin ba.