A tsawon kwanaki 602 a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa a yankin Zirin Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da yakin da suke yi na kisan kiyashi a zirin Gaza, inda suka sake kaddamar da wani sabon yaki kan Gaza bayan tsagaita bude wuta. Hakan ya biyo bayan sauya ra’ayi da Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, bisa la’akari da goyon bayan siyasa da na soji da Amurka ke ba shi, a cikin shiru da kasashen duniya suka yi da kuma gazawar da ba a taba gani ba daga kungiyoyin kasa da kasa.
Kafofin yada labaran Falasdinu sun ruwaito cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da jerin hare-hare ta sama kan yankunan Gaza, da nufin tsaurara tasirin hana shigar da kayan abinci da ya karu tun farkon watan Maris. Wannan ya ba da mummunan hoto na yunwar da mazauna Gaza ke fuskanta.
A safiyar yau Juma’a, jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da wani mummunan farmaki kan yankunan kudancin Khan Yunus. Kamar yadda sojojin na Isra’ila suka yi luguden wuta kan sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Bureij da ke arewacin zirin Gaza da kuma arewa maso yammacin Rafah.