A jiya Talata dai sojojin na kasar Lebanon sun isa a yankin “Ra’asu-Nakurah’ da “Alamus-sha’ab’, bayan da sojojin mamayar HKI su ka janye daga cikinsu.
Bugu da kari sojojin na Lebanon sun isa yankunan “Beit-Lif” da Dhair- Harfa”. A garin Bintu-Jubail ma dai sojojin mamayar na HKI sun janye, da hakan ya bayar da dama ga sojojin Lebanon su ka shiga ciki.
Tun a jiya Talata ne dai sojojin kasar ta Lebanon su ka fara isa duk wasu yankunan da sojojin mamayar su ka janye daga cikinsu.
A wata sanarwar da rundunar sojan kasar ta Lebanon ta fitar ta bayyana cewa, sojojin za su cigaba da shiga yankin Nakura, kuma suna suna kokarin gano abubuwa masu fashewa da ‘yan mamaya su ka bari, ta hanyar aiki tare da rundunar shimfida zaman lafiya ta MDD, (Unifil), da kuma kwamitin bangarori biyar dake sa ido akan tsagaita wutar yaki.
Rundunar sojan kasar ta Lebanon dai ta yi kira ga ‘yan kasar fararen hula da su nesanci shiga cikin wadannan yankunan har zuwa lokacin da sojojin za su gama shiga cikinsu.
A wani labara mai alaka da wannan, shugaban gwamnatin Lebanon Najib Mikati ya bayyana cewa, ya fadawa dan sakon Amurka wajabcin ganin Isra’ila ta dakatar da keta tsagaita wutar yaki. Haka nan kuma ya kara da cewa, sun fada wa dan sakon na Amurka cewa, cigaba da zaman sojojin Isra’ila a cikin kasar Lebanon bayan gushewar kwanaki 6 daga tsagaita wutar yaki, ba abu ne da za a laminta da shi ba.
A bisa yarjejeniyar da a ka cimmawa ta tsagaita wutar yaki, dole ne Isra’ila ta janye sojojinta daga dukkanin wuraren da ta shiga a kudancin Lebanon kwanaki 60 daga tsagaita wutar yaki.