Babu tsaro a Gaza daga laifuka da kisan kiyashin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, sakamakon matakin da Amurka da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka dauka na ayyana wasu wurare a matsayin masu aminci da tsaro, amma Falasdinawa da suka fake a yankunan suna ci gaba da fuskantar luguden bama-bamai daga jiragen saman yaki.
Rahotonni sun bayyana cewa: An samu bullar wasu sabbin kisan kiyashi guda biyu da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a arewaci da tsakiyar Zirin Gaza, ta hanyar yin luguden wuta kan fararen hula da suka rasa matsugunansu suka koma rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira.
Rahotonnin sun bayyana cewa: An samu shahidai da dama da kuma jikkata a wani hare-haren da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wani gida da ke Beit Lahiya da ke arewacin Zirin Gaza, inda suka bayyana cewa, adadi mai yawa na wadanda suka jikkata sun kasance a karkashin baraguzan gine-gine, sannan kafin haka, an kai wasu hare-haren bama-bamai kan wani gida a Tal al-Zaatar a sansanin Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza.