Babban kwamandan sojan Kasa na Iran Janar Abdurrahim Musawi ya bayyana cewa; Sojojin kasar suna cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar duk wata barazana.
Da yake jawabi a wurin bikin makon “Raya Nazari Da Bincike” na jami’ar aikin soja, a jiya Litinin, janar Musawi ya kira yi al’ummar Iran da su kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali domin sojojin suna cikin shiri, sannan ya kara da cewa, Ba da sojoji kadai Iran take dogaro ba, ita ce kasa kadai a duniya irinta wacce take dogaro da dukkanin al’ummarta wajen kare kasa.