Sojojin kasar Iran sun kammala atisayen hadin giuwa mai suna Zolfaghar 1403 a jiya Talata tare da faretin sojojin Ruwa na kasar.
Atisayen ya hada sojojin sama da na ruwa ne, saboda jarraba yadda bangarorin biyu zasu yi aiki tare a lokacin yaki, duk da cewa ko wani bangare yana aiki a inda ya kore, ya ke kuma da masaniya a kansa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin zasu hada kai don tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu cikin ruwa da kan tudu tare.
Manya-manyan kwamandojin sojojin kasar wadanda suka hada da Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin babban kwamnadan sojojin kasar a bangaren tsare-tsare. Da kuma Manjo Janar Abdulrahim Musavi babban kwamandan sojojin kasar iran.
Atisayen ya hada rawar daji a karkashin ruwa don gwada aiki da makamai, da kuma tudun ruwa shi ma don gwada makaman da ake da su. Sannan da yadda za’a yi rundunonin su yi aiki tare, idan bukatar haka ta taso.