Sojojin Iran Sun Ce A Shirye Suke Su Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana Ga Tsaron Kasar

Kwamandan sojojin kasa na JMI Laftanar-Janar Kiyomars Haydari ya bada sanarwan cewa; A bisa umranin jagoran juyin musulunci Imam Sayyid Ali Khamnei , sojojin kasa

Kwamandan sojojin kasa na JMI Laftanar-Janar Kiyomars Haydari ya bada sanarwan cewa; A bisa umranin jagoran juyin musulunci Imam Sayyid Ali Khamnei , sojojin kasa na JMI suna cikin shirin ko ta kwana domin mayar da martani akan kowace irin barazana ga tsaron kasar.

Laftanar janar Haidari ya kuma ce: A halin yanzu da akwai rundunoni 11 da su ke cikin shiri a kan iyakoki kasar domin sanya idanu da tattara bayanai saboda tabbatar da tsaron kasar.

Kwamandan sojan kasa na Iran ya kuma ce; Saboda sojojin suna cikin shirin ko-ta-kwana ne, barazanar da ake fuskanta ta zagwanye, da hakan ya ke a matsayin kandagarko.

Har’ila yau Laftanar janar Haidari ya yi ishara da rawar dajin da sojojin kasa su ka yi, har sau uku a cikin shekarar hijira Shamshiyya ta 1403. Sannan da wadanda za su a sabuwar shekara da za ta shigo.

Ya ce za’a gudanar da wani atisayen wanda zai da ce da girman barazanar da ake fuskanta.

Haidari ya kammala da cewa a sabuwar shekarar Iran da za a shiga, za ta zama ta kara yawan karfin tsaron kasar ne, domin takawa makiya birki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments