Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Yi Wa Falasdinawa Kisan Kiyashi A Rannakun Bikin Babbar Salla

A rana ta biyu tabukuwan  babbar salla, sojojin HKI suna ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyasahi da kuma rusa matsugunansu a yankin Gaza.

A rana ta biyu tabukuwan  babbar salla, sojojin HKI suna ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyasahi da kuma rusa matsugunansu a yankin Gaza.

A yau Asabar kadai gwamman Falasdinawa ne su ka yi shahada a cikin sansanonin da Falasdinawa suke gudun hijira a cikinsu.

An sami shahidai 5  da kuma wasu mutane  biyu da su ka jikkata a kusa da cibiyar rana kayan agaji a yammacin Rafah dake kudancin zirin Gaza.

A yammacin birnin Khan-Yunus kuwa wasu Faladinawa 12 ne su ka yi shahada, yayin da wasu 40 su ka jikkata saboda harin da ‘yan sayahoniyar su ka kai wa sansaninsu.

A arewacin Khan-Yunus kuwa, sojojin mamayar sun ruguza gidajen Falasdinawa da dama.

A kusa da cibiyar kiwon lafiya ta ” Majma’u -Shifa” dake yammacin birnin Gaza, adadin shahidai ya kai 7 wasu biyu kuwa su ka jikkata.

Daga lokacin da HKI ta shelanta yaki akan mutanen Gaza a 2023, adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 54,677, yayin da wadanda su ka jikkata su ka kai 125,530.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments