Da safiyar yau Talata mazauna yankin “al-Daraj’dake Gaza su ka farka daga bacci cikin sanadiyyar harin da jiragen yakin HKI su ka kai wa makarantar ” Musa Bin Nusair” dake karkashin hukumar agaji ta UNRWA” wacce take kunshe da daruruwan ‘yan hijira.
Dama dai wannan ba shi ne karon farko da wannan yankin yake fuskantar hare-hare daga HKI ba.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; Harin na yau ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 44,mafi yawancinsu mata ne da kananan yara, baya ga wani adadi mai yawa na Falasdinawan da su ka jikkata.
Kananan yara da suke rayuwa a cikin wannan sansanin ‘yan hijira sun rika kai da komowa suna neman kayan wasanninsu daga karkashin baraguzai.
A kusa da asibitin “Ma’amadani” wanda sojojin sahayoniyar su ka kashe mutane 500 a cikinsa, tun farko-farkon yaki, an ga wasu mata suna bak kwana da dangi da ‘yan’uwansu da su ka yi shahada cikin kuka mai kuna.
Tuni dai aka yi jana’izar jam’i ta shahidan su 44.
Yakin Gaza dai ya shiga watanni na 18, ta yadda a halin yanzu babu wani wuri mai rufi idan ba hemomin da ‘yan hijira suke ciki ba. Bugu da kari sojojin na HKI sun lalata dukkanin muhimman cibiyoyin yankin na Gaza, da su ka hada na samar da ruwa, wutar lantarki, da kuma hana shigar da kayan abinci da magani cikin yankin.