Sojojin HKI sun kai sumame a sansanin yan gudun hijira na Balata dake kusa da birnin Nablos a yankin yamma da kogin Jordan a safiyar yau Alhamis.
Kamfanin dillancin labaran Mehra na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun kama Falasdinawa biyu sun tafi da su a yayinsa suka jiwa wani guda rauni tare da harba albarushi a kansa.
Labarin ya kara da cewa banda sansanin yan gudun hijira na Balata, sojojin yahudawan sun kai sumame a garuruwan Asirah, Atil, Zatya da Qafin daga arewacin Tulkaram. Sannan sun kai sumame a yankin Dawaar na garin Qalqeliya.
A wani labarin kuma kungiyar ‘likitocin da babu iya’ ta bada sanarwan cewa asbitin Nasir dake garin Khan Yunus a yankin zirin gaza ya na daf da dakatar da aiki saboda karancin makamashin bada wutan lantarki.