Jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan arewacin Gaza a daren jiya inda suka kai Falasdinawa da dama ga shahad sun kuma jefa boma-bomai a kan wasu makarantu da asbitocin da Falasdinawan suke samun mafaka a cikinsu.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza na fadar cewa a safiyar yau Lahadi jiragen yakin HKI sun kai falasdinawa 8 ga shahada, a makarantar Musa bin Nusair inda iyalai da dama suke samun mafaka.
Banda haka yahudawan sun kai hare-hare kan asbitin Al-Awda dake sansanin yan gudun hijira na garin Jabalia. Har’ila yau sun raunata falasdinawa a asbitin kamal Adwan a beit Lahiya.
A asbitan Awda sojojin yahudawan sun yi amfani da makaman Atilary a haren nasu. Sun kuma yi amfani da masu amfani da bindigogi mai kashe mutum guda daga nesa. wato (Snipers).
Wasu hotunan asbitin kamal adwan sun nuna marasa lafiya kwance a kasa a barandar asbitin saboda rashin gadajen da kuma wuraren da suka da ce da marasa lafiya.
Dr. Hussam Abu Safiya shugaban Asbitin ya bayyana cewa yahudawan sun kaiwa asbitinsa hare hare ne ba tare da gargadiba, sannan sun yi amfani da makamai daban-daban a hare-haren.