Sojojin HKI Kimani 40 Ne Suka Halaka Ko Suka Jikata A Jiya Jumma’a A Yankin Shuja’iyya Na Birnin Gaza

Kungiyar Falasdinawa ta Jihadul Islami a Gaza, ta bada sanarwan halaka ko jikatar sojojin yahudawan Sahyoniyya 40 a gaza a wani tarko mai sarkakiyan da

Kungiyar Falasdinawa ta Jihadul Islami a Gaza, ta bada sanarwan halaka ko jikatar sojojin yahudawan Sahyoniyya 40 a gaza a wani tarko mai sarkakiyan da suka dana masu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Saraya Qudus” reshen soje na kungiyar Jihadul Islamim yana fadar haka a jiya Jumma’a.

Daya daga cikin kwamnadojin dakarun ya bayyana cewa da farko halakar yahudawan ta faru ne a garin Gaza a kuma unguwar shuja’iyya. Inda da farko suka halaka sojojin yahudawa kimani 10 a cikin wani ginin da suka shiga cikinsa tare da amfani da makamai mai linzami, sannan a wani gidan

Sannan waso sojojin kimani 20 sun halaka ko sun ji rauni a lokacin dakarun suka yi am,fani da makamin TBG wanda yake watsa isakar gas da ruwa da kuma gari a inda ya fashe don kona jikin wadanda ya fashe a cikinsu.

Na uku kuma sun tana nakiyoyi masu karfi kan tankar yaki dauke da akalla sojojin yahudawa 6 suka kone .

Labarin ya kara da cewa sojojin makiya a irin wannan halin sun kasa daukar wani mataki in banda gudu daga wurin. Daga karshe ba abinda zaka gani sai gawakin sojoji a waste a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted