Hare-haren wuce gona da irin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suke kai wa kan Gaza sun janyo rushewar ayyukan jinya a birnin
Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na ci gaba da yin ruwan bama-bamai a kan birnin Gaza, lamarin da ke kara janyo cikas ga ayyukan jinya tare da kara radadin Falasdinawa.
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya ce: Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan shiyar arewacin Zirin Gaza, yayin da farmakin da sojoji ke kai wa kan birnin bai tsaya ba, kamar yadda suke ci gaba da kai hare-haren bama-bamai kan hasumiyoyi da gidajen zama Falasdinawa, lamarin da ya kara kaimin rushe-rushe da karin wahala da kuma damuwa ga al’umma.
Ya kara da cewa ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan kudu maso yammacin birnin Gaza, da unguwar Rimal da jami’a da Tal al-Hawa, da kuma al-Sina’a.