Sojojin Faransa Sun Fara Ficewa Daga Chadi Bayan Kawo Karshen Yarjejeniyar Da Kasashen Biyu Suka Cimma

Sojojin Faransa sun fara ficewa daga cikin kasar Chadi a matakin da gwamnatin Chadi ta dauka na korar sojojin Faransa daga kasarta Ma’aikatar harkokin wajen

Sojojin Faransa sun fara ficewa daga cikin kasar Chadi a matakin da gwamnatin Chadi ta dauka na korar sojojin Faransa daga kasarta

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Chadi ta sanar da aiwatar da matakin farko na mayar da sojojin Faransa zuwa kasarsu da aka jibge a cikin kasarta, wannan na zuwa ne bayan ficewar jiragen yakin Faransa daga cikin kasar, bisa la’akari da cewa: Wannan lamari yana matsayin wani babban mataki ne na aiwatar yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu kuma wa’adinsa ya zo karshe.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Chadi ta fitar ta ce: A ci gaba da aiwatar da matakin da gwamnatin Jamhuriyar Chadi ta dauka na aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwar aikin soji da Faransa, inda bayan karewar yarjejeniyar ta bukacin ficewar sojojin Faransa daga kasarta ba tare da bukatar sake tsawaita yarjejeniyar ba.

Sanarwar ta kara da cewa: Wannan lamari yana wakiltar wani babban mataki ne na aiwatar da jadawalin da bangarorin biyu suka amince da shi, kuma sojojin Faransar za su ci gaba da janyewar bisa sharuddan da aka cimma sannu a hankali cikin makonni masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments