Sojojin Amurka sun kammala janyewa daga Nijar gaba daya

An kammala aikin janyewar sojojin Amurka daga Nijar, kamar yadda wani jami’in Amurka ya sanar a wannan Litinin. A watan da ya gabata, Amurka ta

An kammala aikin janyewar sojojin Amurka daga Nijar, kamar yadda wani jami’in Amurka ya sanar a wannan Litinin.

A watan da ya gabata, Amurka ta mika ragowar sansanonin soji ga hukumomin Nijar,

A cikin watan Maris ne dai gwamnatin Nijar ta soke yarjejeniyar da ta bai wa sojojin Amurka damar gudanar da ayyukansu a kasar, inda jami’an kasashen biyu suka fitar da sanarwar hadin gwiwa bayan ‘yan watannin da suka gabata, inda suka sanar da janyewar a tsakiyar watan Satumba.

Kafofin yada labaran kasar Nijar sun bayar da rahoto a baya a cikin watan Disamba na shekarar 2023, inda suka ambaci batun  wata wasika daga ma’aikatar harkokin wajen Nijar zuwa ga wakilan diflomasiyya na kasashen da ke da sansanonin soji a Yamai, cewa gwamnatin Nijar na shirin bayyana shirin sake duba yarjejeniyoyin soja da aka kulla da kasashen yammacin Turai a baya.

A cewar wasikar, wannan matakin wata alama ce ta sadaukarwarsu da kuma kare muradun da bukatun al’ummar Nijar.”

Ta kara da cewa, “Za a mika musu daftarin yarjejeniyar fahimtar juna zuwa ga kasashen abokan hulda da ke da rundunar soji da aka jibge a yankin Nijar, don farfado da sabuwar rayuwa ga hadin gwiwar bangarorin biyu.”

A watan Afrilu,  masu horas da sojoji sun iso ne daga kasar Rasha domin karfafawa da kuma inganta tsaron sararin samaniyar Nijar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments