Search
Close this search box.

Siriya: Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare Hare A Kan Wasu Wurare A  Birnin Damascus Babban Birnin Kasar

Jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan wasu sasanonin sojojin kasar Siriya a kusa da babban birnin kasar Damascus a darin Talata. Tashar talabijin

Jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan wasu sasanonin sojojin kasar Siriya a kusa da babban birnin kasar Damascus a darin Talata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar na fadar cewa jiragen yakin na HKI sun fito ne daga yankin tuddan Golan na kasar Siriya da ta mamaye, kuma sai kai hare haren da misalign karfe 2.10 na daren Talata.

Labarin ya kara da cewa hare haren sun jawo barna da dukiyoyi a wadannan wurare amma babu wanda ya ji ko korzone daga cikin jami’an tsaron da suke a cikin wadannan wurare.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa garkuwan makamai masu linzami na sojojin kasar sun sami nasarar kakkabo wasu daga cikin makaman da jiragen yakin HKI suka cilla a kan wadannan sansanonin sojoji.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments