Shugabannan Palasdinawa daga cikin har da kungiyar Hamas da Jahadul Islami duk sun ki amincewa da shirin trump na sake kwace Gaza, kafin haka kuma shugaban ya ce dole Falasdinawa su daga yankin kafin ya kwace shi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shuwagabannin Palasdinawan suna allawadai da shugaban, sun kuma kara da cewa abinda HKI bata samu da yakin wattnin 15 ba, shugaba Trump ya na ya ba su da sauki da kuma wayon da za’a yiwa yaro.
A ranar talata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai kwace Gaza a hannun Palasdinawa sannan ya sake gina shi.
Falasdinawa kimani 61,700 suka rasa rayukansu a yayin da fiye da 100,000 ji rauni a yakin watanni 15 da suka fafata da HKI a Gza..