Search
Close this search box.

Kawancen Masu Gwagwarmaya Sun Tabbatar Da Cewa HKI Ba Zata Sami Nasara A Yakin Tufanul Aksa Ba

Shugabannin kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a kasashen larabawa wadanda suke halattan taron kasashen larabawa karo na 33 a birnin Bierut babban kasar Lebanon sun

Shugabannin kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a kasashen larabawa wadanda suke halattan taron kasashen larabawa karo na 33 a birnin Bierut babban kasar Lebanon sun bayyana cewa shuwagabannin HKI duk tare da taimakon kawayenta na kasashen yamma ta kasa kaiwa ga manufofinta a yakin tufanul Aksa.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa ana gudanar da taron a wannan karon ne da sunan ‘Zamanin Tufanul Aksa’. Kuma taron na kwanaki

Shuwagabannin kasashen larabawa masu gwagwarmaya sun bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ta sauya al-amura a yankin, kuma an shiga wata marhala daban a yankin da kuma duniya gaba daya.

Banda haka sun yi kira ga shuwagabannin kasashen larabawa wadanda suke tunanin samar da hulda da HKI su ijiye wannan batun su kuma goyi bayan falasdinawa masu gwagwarmaya don ganin bayan HKI a yankin.

Shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya wanda ya gabatar da jawabin da aka dauka da hoton bidiyo, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa, ta mai al-amarin masu gwagwarmaya wata marhala babba, kuma hakan ya samu ne saboda juriya da kuma turjiyar mutanen gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments